✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin sojoji ta sama ya kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji ce ta kai harin ta sama

Akalla ’yan ta’adda 82 ne wasu hare-haren sojojin sama suka kashe a yankin Rafin Dankura da ke Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Sun gamu da karar kwanan ne lokacin da suke kokarin satar mutanen yankin, inda suka yi arangama da dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji.

Hedkwatar Tsaro ta kasa ce ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Daraktan yada labarai na hedkwatar, Manjo Janar Benard Onyeuko, lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani, ya kuma ce ’yan ta’adda 4,770 sun mika wuya a Jihar Borno daga tsakanin 16 zuwa 30 ga watan Yunin 2022.

A cewarsa, a ranar 22 ga watan Yunin 2022, bangaren sojojin sama na Operation Hadarin Daji ya kai hari ta sama a kauyen Kofar Danya da ke Karamar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.

Ya ce an kaddamar da harin ne bayan samun bayanai cewa ’yan ta’addan na shirin kai farmaki kauyen.

Manjo Janar Benard ya ce nan take dakarun suka yi wa wajen dirar mikiya, inda suka iske ’yan ta’adda sama da 150 a cikin daji.

“A sakamakon harin, majiyoyi daga yankin na Kofar Danya sun tabbatar mana cewa mun kashe ’yan ta’adda sama da 82, wasu kuma da dama suka ji munanan raunuka,” inji shi.

Ya ce bayan harin, sojojin sun sami nasarar kubutar da mutum shida da aka yi garkuwa da su, sun kashe ’yan bindiga biyu sannan sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da wata bindigar kirar gida guda daya da wayoyin salula guda biyu da kuma tsabar kudi N211,915.