✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin sojojin sama ya kashe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa

Rundunar Tsaro ta Operation Lafiya Dole ya karkashe ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a maboyarsu dake Njima da Dure a dajin Sambisa

Shalkwatar Tsaro ta Kasa ta ce hare-haren dakarun Rundunar Tsaro ta Operation Lafiya Dole ya karkashe ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a maboyarsu dake Njima da Dure a dajin Sambisa dake jihar Borno.

Jami’in sashen dake samar da bayanai kan ayyukan rundunar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce rundunar na ci gaba da samun gagarumar nasara a yakin da take yi da ‘yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.

Manjo Janar Enenche ya ce sun kai harin na baya-bayan nan ne ranar Talata bayan jiragensu na sama sun gano maboyar ‘yan ta’addan a wuraren guda biyu.

A cewarsa, jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya sun tarwatsa maboyar mayakan kungiyar tare da yi musu barna mai yawan gaske.

“Rundunar Sojoji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakin da take yi har sai ta kakkabe dukkan ‘yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da suke fama da rikici,” inji Enenche.