✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Taliban ya hallaka jami’an tsaron Afghanistan 8

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wani harin kunar bakin wake da ya hallaka jami’an tsaro takwas a kasar Afghanistan.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wani harin kunar bakin wake da ya hallaka jami’an tsaro takwas bayan wani hari da aka kai kusa da sansanin shalkwatar tsaron kasar Afghanistan.

Dan kunar bakin waken dai ya tashi motar da yake tukawa wacce ke cike da bama-bamai a ranar Asabar a yankin Nangarhar.

Harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan Hukumar Tsaron Amurka ta Pentagon ta zargi Taliban din da kin mutunta yarjejeniyar da suka cimma a birnin Washington a bara, ciki har da yanke dukkan alaka da kungiyar Alka’ida.

Mataimkin Magajin Garin Nangarhar, Ajmal Omar, ya tabbatar da faruwar hatsarin, ko da yake ya ce sojojin da suka mutu sun kai 15, yayin da karin wasu biyar kuma suka jikkata.

Kakakin kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid ya ce kungiyarsa ce ta kai harin.

A wani labarin kuma, Ofishin Gwamnan yankin ya ce jami’an tsaro sun kuma kwace wata mota shake da abubuwan fashewa a kusa da birnin Jalalabad babban birnin jihar ta Nangarhar.

Yankin dai a ’yan kwankin nan ya yi ta fuskantar munanan hare-hare wadanda kungiyar ISIL ta dauki alhakin kai su.

An dai yi ta fuskantar rikice-rikice da hare-hare iri-iri a kasar, duk kuwa da cewa kungiyar Taliban da gwamantin kasar sun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwambar bara.

Ya zuwa yanzu dai ba a ga wani tasiri daga yarjejeniyar ba.