Daily Trust Aminiya - Harshen Hausa hantsi ne –Farfesa Dangambo
Dailytrust TV

Harshen Hausa hantsi ne –Farfesa Dangambo

Ranar 26 ga watan Agusta ce Ranar Hausa ta Duniya.
A da a kafofin sada zumunta akan yi bikin wannan Rana, amma a baya-bayan abin ya faɗaɗa har tarurruka da sauran shagulgula ake yi a garuruwa da kasashe daban-daban na duniya.

A wannan hirar da Sani Ibrahim Paki ya yi da shi Farfesa Abdulkadir Dangambo, masani kuma fitaccen malamin Hausa, ya fadi abin da ya sa harshen ya cancanci a ware rana guda domin shi.