✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsari: Mutum 7 sun mutu, wasu 5 sun jikkata a hanyar Legas

Mutum bakwai sun mutu nan take bayan afkuwar hatsarin.

Akalla fasinja bakwai ne suka mutu yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wani hatsari da wata motar bas ta yi taho mu gama da wata motar dakon kaya a kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Bayanai sun nuna cewa shi wannan hatsari ya faru ne da misalin karfe 7:40 na dare kusa da ofishin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da ke kan babbar hanyar.

Wata motar bas kirar Mazda mai lamba LSR696XS ta afka wa wata babbar mota mai lamba T-4889LA, inda mutane bakwai suka mutu nan take.

Kakakin hukumar FRSC, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar hatsarin a daren ranar Juma’a, inda ta ce motar din na dauke da fasinjoji 16; maza 15 da mace guda daya.

Ta ce sun samu rahoton mutuwar mutum bakwai, ciki har da mace daya tilo da ke cikin bas din.

Okpe, ta bayyana cewa mai yiwuwa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu da kuma rashin kula da direban bas din ya yi.

Kazalika, an kai wadanda suka ji raunin zuwa Asibitin Nasara da ke Ogere, domin ba su agajin gaggawa yayin da aka ajiye gawar wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na FOS da ke Ipara.

Kakakin ta ce Kwamandan hukumar, Ahmed Umar, ya bayyana hatsarin a matsayin abin da za a iya guje wa faruwarsa, idan direban ya bi ka’ida, saboda ana ruwan sama a lokacin hatsarin ya faru.

A cewarta, Kwamandan ya yi gargadi kan yadda masu ababen hawa ke keta gudu ba gaira babu dalili.

Har wa yau, ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, sannan ya bukaci su da su tuntubi hukumar da ke yankin Ogunmakin domin samun karin bayani kan lamarin.