✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsari ya yi ajalin mutum shida a hanyar Sagamu

Hatsarin ya auku ne sakamakon kuskuren wuce abokin tafiya da kuma gudun wuce sa’a.

Rayukan mutum shida ne suka salwanta sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku daren Litinin a Jihar Ogun.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra reshen Jihar, Mista Ahmed Umar, ya ce hatsarin wanda ya ritsa da motoci uku ya auku ne a kan babbar hanyar Sagamu zuwa Benin.

Mista Umar ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12.01 na dare inda aka samu akasi wata babbar motar fasinja ta yi kuskuren wuce abokin tafiya da kuma gudun wuce sa’a.

A cewarsa, mutane 39 ne hatsarin ya ritsa da su, wadanda suka hada maza 25 da mata 14, kuma daga ciki maza biyar da mace daya suka riga mu gidan gaskiya.

“Babbar motar fasinjar ce ta daki mota kirar Sienna da kuma Mazda” in ji shi.

“Nan take direban motar ya gudu saboda dukkan fasinjojin cikin Sienna sun mutu yayin da na cikin Mazda suka ji raunika.”

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito Mista Umar yana cewa, an jibge gawar wadanda aka rasa a Babban Asibitin Ijebu Ode, inda kuma a nan ne ake duba lafiyar mutum hudu da suka jikkata.