✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin Bagwai: ‘Har yanzu muna neman gawarwakin mutum 14’

Gwamnatin ta ce ana ci gaba da bincike don gano ragowar da suka bace.

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 29 a hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Karamar Hukumar Bagwai a ranar Talata, yayin da mutum 14 suka bace.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Laraba.

“Mutum bakwai na babban asibitin garin Bichi inda ake kula da su, yayin da kuma mutum 14 suka bace amma ana ci gaba da bincike,” inji shi.

Kazalika, ya ce daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su, mata da kananan yara sun fi yawa.

Ya ce gwamnatin Jihar ta kafa kwamiti na musamman don gudanar da bincike kan yadda hatsarin ya faru tare da gujewa faruwar hakan a nan gaba.

Garba, ya ce kwamitin da aka kafa na karkashin jagorancin Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa da ke Jihar, Kaftin Muhammad Abubakar-Alhassan.

Har wa yau, ya ce daga cikin mambobin kwamitin akwai Kwamishinan Yada Labarai da na Harkokin Addini, da na Kananan Hukumomi da na Gidaje da Sufuri na Jihar.

Sai kuma karin shugabannin ’yan sanda, DSS, NSCDC, NEMA da sauransu.

Ya ce gwamnatin Jihar ta yi alkawarin sayen manyan jiragen ruwa don inganta harkar sufuri a yankin.

Garba, ya ce tuni gwamnatin ta fara rabon 100,000 ga iyalan wadanda suka rasa iyalansu a sanadin hatsarin.

A cewarsa, za a raba buhu 120 na Shinkafa, Masara, Dawa, Gero ga wadanda abin ya shafa.

Ya sake bayyana cewar gwamnatin ta ba wa Hukumar Sufuri ta Jihar umarnin yin jigilar mutanen yankin a motoci guda biyu har na tsawon wata guda kyauta.