✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin kasa ya yi ajalin mutum 11 a Masar

Akalla rayukan mutum 11 ne suka salwanta yayin da 98 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku ranar Lahadi a garin…

Akalla rayukan mutum 11 ne suka salwanta yayin da 98 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku ranar Lahadi a garin Toukh da ke Arewacin kasar Masar.

Sanarwar da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta fitar ta bayyana cewa, motocin agaji sittin aka turo domin kwaso gawawwaki da wadanda suka jikkata kuma aka garzaya da su wasu manyan asibitoci uku da ke Cairo, babban birnin kasar.

Hatsarin ya faru ne yayin da tarago hudu na jirgin suka sauka daga layin dogo daf da garin Mansoura bayan ya baro birnin Cairo kamar yadda Ma’aikatar Sufurin kasar ta bayyana.

Shugaban Kasar, Abdel-Fattah al-Sisi ya bayar da umarnin kafa wani kwamitin gaggawa domin bin diddigi a kan musabbabin aukuwar hatsaron.

A halin yanzu dai bincike ya kankama, inda direban jirgin tare da mataimakinsa da wasu jami’ai takwas na tashar Toukh ke shigar da bayanai a ofishin shari’a na kasar.