✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin jirgin ruwa ya kashe mutane a Kano

An yi nasarar ceto mutum biyu, yayin da mutum biyu kuma suka rasa rayukansu.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum biyu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Durgu na Karamar Hukumar Rimin Gado ta jihar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ya ce hukumar ta kuma yi nasar kubutar da wasu mutum biyu da hatsarin na ranar Litinin ya rutsa da su.

“Mun samu kiran agaji daga wani Munir Dahiru a misalin karfe 11:50 na safe, cewa wani kwalekwale ya nutse a ruwa.

“Bayan samun kiran, nan take muka aike da jami’anmu zuwa wajen da misalin karfe 12:30 kuma an fito da wadanda hatsarin ya rutsa da su,” a cewar sanarwar.

Ya ce mutum biyu da suka rasu su  ne Sha’aban Bala mai shekara 35 da Rabiu Bashari mai shekara 30; Sai mutum biyu da aka ceto kuma, Sani Shitu mai shekara 25 da kuma Jabir Sani mai shekara 30.

Abdullahi ya ce mutanen sun shiga kwalekwalen da nufin zuwa kauyen Kanya daga Zangon Durgu.

“An mika gawar wadanda suka rasu ga Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Shafiu Abdullahi Gulu; Ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin,” in ji shi.