✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum 13 a Sakkwato

Hatsarin ya auku bayan kwanaki 9 da aukuwar makamancinsa a Jihar Kebbi.

Mutum 13 ne suka rasu dukkansu mata da kananan yara a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Alhamis a Karamar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda lamarin ya riutsa da su sun taso ne daga kauyen Doruwa zuwa Dinga yayin da jirgin ya nutse da su ciki har da maza dattawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Dantine Shagari, ya ce tuni aka yi jana’izar wadanda suka rasu da suka hada da mata 8 da kananan yara biyar.

Alhaji Dantine ya alakanta aukuwar hatsarin da yi wa jirgin lodin nauyin da ya wuce kima.

Ya ce, “Amma akwai wasu dalilai da ka iya janyo hatsarin ciki har da iska mai karfi, kuma muna ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin aukuwar hatsarin.”

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya jajanta wa ’yan uwan wadanda lamarin ya shafa, inda ya sha alwashin samar wa da al’ummomin yankin jiragen ruwa masu amfani da inji da kuma rigunan hana nutsewa a ruwa don kaucewa faruwar hakan a gaba.

Kazalika, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana kaduwarsa dangane da rasuwar mutum 13 a hatsarin, inda ya yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan hatsari ya auku bayan kimanin kwanaki 9 da aukuwar makamancinsa a Jihar Kebbi wanda ya yi sanadiyyar rayukan fiye da mutum 100.

Ana iya tuna cewa, a bara ce mutane 9 suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin jirgin ruwa da ya rutsa da su yankin Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.