✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: Majalisa ta tallafa wa iyalai da N10m

Majalisa ta bayar da tallafin ga iyalan ta hannun Masarautar Yauri.

Majalisar Dattijai ta ba da tallafin Naira miliyan 10 ga iyalan da hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a garin Warrah na Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.

Da yake sanar da ba da tallafin a Birnin Kebbi a ranar Juma’a, Sanata  Adamu Aliero, wanda ya jagoranci ayarin domin jajanta wa Gwamna Atiku Bagudu kan hatsarin jirgin, ya ce za a hannunta tallafin ne ga Masarautar Yauri a madadin iyalan da abin ya shafa.

“Za mu je Masarautar Yauri domin ba da tallafin ga iyalan da lamarin ya shafa.

“Majalisar Dattijai ta damu matuka da faruwar hadarin kuma za ta tabbatar da hukumar kula da ruwa ta cikin Najeriya (NIWA) ta dauki matakan kare faruwar hadura a nan gaba,” inji shi.

Aliero ya ce Majalisar za ta tabbatar da Hukumar ta kawar da kututturan bishiyoyi da manyan duwatsun da suke haddasa hadurra irin wadannan.

Ya ce Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Dokta Abdullahi Yahaya, shi ne ya gabatar da kudurin duba batun a zauren, sannan ya samu goyon bayan takwaransa Sanata Adamu Aliero.