✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin sama ya yi ajalin mutum 67 a Nepal

Jirgin dai na dauke ne da mutum 72

Akalla mutum 67 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani hatsarin jirgin sama da ya auku a kasar Nepal ranar Lahadi.

’Yan sandan kasar sun ce hatsarin wanda ya auku a yankin Himalaya a cikin jirgin da ke dauke da mutum 72, shi ne irinsa mafi muni a kasar cikin sama da shekara 30.

“Akwai gawarwaki 31 da aka garzaya da su asibiti,” in ji AK Chhetri, jami’in dan sanda a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya kuma ce har yanzu akwai mutum 36 da ake neman su bayan wani sashe na jirgin ya fada cikin wani rami.

Shi ma Kakakin Rundunar Sojojin Kasar, Krishna Prasad Bhandari, ya ce an sami nasarar ceto gawarwaki 29, sannan akwai karin wasu 33 a ramin da jirgin ya fada a yankin Phokara da ke tsakiyar kasar ta Nepal.

Jirgin dai wanda ya taso daga Kathmandu babban birnin kasar ya fadi ne a cikin wani rami inda ya kakkarye, a dab da sabon filin jirgin sama na Phokara, wasu ’yan mintuna kafin karfe 12:00 na ranar Lahadi, a agogon Najeriya.

Jim kadan da faruwar hatsarin ne ma’aikatan ceto suka dukufa aiki, yayin da hayaki ya turnuke wajen, ga kuma daruruwan mutane da suka baibaye wajen suna kallo.

Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta, wadanda bisa ga dukkan alamu an dauke su ne bayan aukuwar hatsarin, sun nuna wasu sassa na jirgin na ci da wuta a kasa, yayin da bakin hayaki kuma ya tirnike wajen.