✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota: Gombawa 17 sun rasu a hanyar zuwa Legas

Bayanai sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce milasali da bas din ta yi.

Mutum 17 da suka taso daga jihar Gombe sun riga mu gidan gaskiya a wani hatsari da ya rutsa da su da sanyin safiyar Talata a babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Aminiya ta kalato wadanda lamarin ya shafa fasinjoji ne da suka shiga mota da nufin zuwa Legas daga Gombe.

An ga jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC), sun garzaya da wadanda suka jikkata a hatsarin zuwa Babban Asibitin Abaji don yi musu magani.

Majiyarmu ta ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe biyar na asuba tsakanin wata bas kirar Toyota mai daukar mutum 18 mai lamba GME 20 XA da kuma wata babbar motar daukar kaya mai lamba BAU 632 XA.

A cewar majiyar, bas din ta fito ne daga yankin Gwagwalada a guje ta daki bayan babbar motar inda nan take ta kama da wuta.

Majiyar ta kara da cewa, hudu daga cikin fasinjoji 21 da ke cikin motar suka tsira, yayin da 17 suka makale suka kuma kone.

Kwamandan FRSC na yankin Abuja, Mista Samuel Ogar Ochi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare dangantar hatsarin da gudun wuce misali.