✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya kashe mutum 19 a Sakkawato

Taho mu gamar ta kashe mutun 19 nan take wasu kuma sun jikkata

Hukumomi a Jihar Sakkawato sun ce mutum 19 sun mutu a wani hatsarin mota a kan hanyar Gusau-Sakkwato.

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwaato, DSP Muhammad Sadiq ya ce motoci biyu ne suka yi taho-mu-gama inda nan take mutun 19 suka mutu, wasu 14 kuma suka samu munanan raunuka.

Ya ce an yi hatsarin ne a kauyen Bimasa da ke Karamar Hukumar Tureta da misalin 4:30 na yamma ranar Alhami.

Hatsarin a cewarsa ya ritsa ne da wata karamar mota kirar Golf mai lambar Sakkwato ta Arewa da kuma Bus kirar Hiace mai lambar Bodinga.

Jami’in ya ce tuni aka kwashi gawarwakin da wadadan da suka jikkatan zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUTH) da ke garin Sakkwato inda suke samun kulawa.