Daily Trust Aminiya - Hatsarin mota ya rutsa da tsohon dan wasa Samuel Eto’o
Subscribe

Samuel Eto’o

Hatsarin mota ya rutsa da tsohon dan wasa Samuel Eto’o

A halin yanzu tsohon dan wasan kungiyar Barcelona Samuel Eto’o, yana kwance a gadon asibiti bayan ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Lahadi a kasar Kamaru.

Kafar watsa labarun kwallo ta Goal.com ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tsohon dan wasan na kungiyar Inter Milan a kan titin Nkpongsamba zuwa Douala yayin da yak e dawo wa daga wani biki da ya halarta a Arewacin Kamaru.

Hatsarin ya auku ne a yayin da wata motar haya kirar Bus ta gwabza wa motar Samuel cikin gaggawa aka garzaya da shi asibiti kuma likitoci suka yi azamar duba lafiyarsa kamar yadda wani dan jarida a kasar Kamaru, Martin Camus ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Martin Camus ya wallafa hoton yadda motar Eto’o ta yi rugu-rugu da cewa dan wasan ya fara murmure wa a yayin da yake ci gaba da samun kulawa ta kwararru na lafiya.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Faransa ta ruwaito cewa, Eto’o mai shekaru 39 a duniya ya samu rauni a kansa, sai dai an taki sa’a babu rai ko daya da ya salwanta a hatsarin.

Eto’o wanda shi ne mashawarci na musamman ga shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika, Ahmad Ahmad, ya sanar da ajiye kwallo a watan Satumba na 2019 bayan ya shafe tsawon shekaru 22 a fagen sana’ar.

.

More Stories