✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 14 a Jihar Kogi

Akalla mutum 14 ciki har da kananan yara biyar ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya auku a tsakanin motoci a yankin…

Akalla mutum 14 ciki har da kananan yara biyar ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya auku a tsakanin motoci a yankin Ojuwa-Olijo da ke babbar hanyar Anyinba zuwa Ajaokuta a Jihar Kogi.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra reshen Jihar, Mista Solomon Aghure, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawarsa da manema labarai a Lokoja, babban birnin Jihar.

Aukuwar hatsarin a ranar Alhamis ta rista da wasu manyan motocin daukan kaya guda biyu da wata motar bas da ke kan hanya daya tare da su kuma ta makale a tsakaninsu.

Alkaluman wadanda suka riga mu gidan gaskiya a hatsarin sun hadar da kananan yara mata uku, yara maza biyu, mata takwas da wani mutum daya.

A cewarsa, maza uku da mace daya da yara biyar – maza biyu da mata uku, sun tsallake rijiya da baya yayin da suka tsira a hatsarin da raunuka kadai.

Ya ce an mika wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Holley Memorial da ke Ochadamu yayin da kuma aka killace wadanda suka riga mu gidan gaskiya a Asibitin Grimard da ke Anyingba.

Mista Aghure ya alakan aukuwar wannan hatsari da rashin birki a daya daga cikin manyan motocin biyu sai dai ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin aukuwar lamarin.

Aminiya ta gano cewa an dauki tsawon lokaci kafin jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra su fara aikin ceton rayukan wadanda hatsarin ya ritsa da su.

Kazalika, an tabbatar da cewa mutum 14 daga cikin 23 da hatsarin ya ritsa da su sun mutu nan take yayin da wasu mutum tara suka samu raunuka iri daban-daban.