✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 16 a Legas

An gano tukin ganganci cikin dare ne ya haddasa hatsarin.

Akalla mutum 16 ne suka mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a safiyar ranar Talata a unguwar Epe da ke Legas.

Mummunan hatsarin ya rutsa da motoci biyu, wata farar bas da wata babbar mota a kan hanyar garin Alaro, a Epe.

An ce motar bas din na dauke da fasinjoji da ke tafiyar tsakar dare daga Legas zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

An gano cewa motar bas din ta afka wa babbar motar ce da misalin karfe 3 na dare saboda rashin ganin hanya yadda ya kamata.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura na kasa (FRSC) reshen Jihar Legas, Olusegun Ogungbemide, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya dora alhakinsa kan tukin ganganci.

Ogungbemide ya shawarci masu ababen hawa da su guji tukin dare, duba da irin hatsarin da ke tattare da hakan da kuma rashin kyawun hanyoyi.

Kwamandan ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka a sanadin hatsarin.