Daily Trust Aminiya - Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4 tare da raunata wasu
Subscribe

Hadarin Mota

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4 tare da raunata wasu

Hadarin mota ya yi ajalin mutum hudu tare da raunata bakwai a a Jihar Kwara.

Hadarin ya faru ne bayan wata bas din haya kirar ‘Toyota Hummer’ ta yi taho mu gama da wata tirela sakamakon gudun wuce ka’ida da direban bas din ke yi a lokacin.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC), reshen jihar Jonathan Owoade, ya ce mutum bakwasi kuma daga cikin 18 da ke cikin motar, sun ji munanan raunuka.

Ya ce hadarin ya faru ne a garin Otte, kusa da babban titin Ilorin-Ogbomoso na zuwa filin jiragen saman da ke Jihar Kwara ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa an kai mutane shida da suka samu raunuka Babban Asibitin Ilorin, sai mutum daya da aka kai Asibitin Eyenkorin, da ke Ilorin.

More Stories