✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 6 a Kwara

Hatsarin ya faru sakamakon ne tukin ganganci.

Akalla mutum shida ne suka rasu a wani hatsarin mota a kan titin Offa zuwa Asaje a Jihar Kwara.

Hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Peugeot 406 mai lamba RBC 424 DW da kuma wata kirar Mazda 323 mai lamba BWR 590 BJ a ranar Alhamis.

An ruwaito cewa motocin biyu sun yi hatsari ne da misalin karfe 2:35 na yamma sakamakon tukin ganganci.

Abin ya rutsa ne da mutum takwas, shida daga ciki, maza biyu, mata biyu da kuma kananan yara biyu suka rasu; Ragowar mutum biyun kuma mace da namiji sun ji rauni.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a Jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya ce wadanda suka rage sun samu karaya da sauran raunuka kuma an kai su su asibiti don ba su agajin gaggawa.

Ya kara da cewa an mika kayayyakin da aka samu a wurin da hatsarin ya afku ga ofishin ’yan sanda na Ajase.

“An mika wadanda suka ji rauni Babban Asibitin Offa don ba su kulawar da ta dace, wadanda suka mutu kuma an ajiye gawarwakinsu,” inji shi.