✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9, ya jikkata 13 a Bauchi

Hadarin ya auku ne a kan titin Postikum zuwa Azare

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutum tara, wasu 13 kuma sun sami raunuka a wani mummunan hatsarin mota a jihar.

Hadarin ya auku ne a daidai garin Kwanan Shettu da ke kan titin Postikum zuwa Azare mai nisan kilomita 22 daga Bauchi.

Hatsarin ya farune tsakanin wata motar tirelar kirar DAF mai lamba KTG 08 XC da wata mota kirar Toyota Hiace ta kasuwanci.

Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da rahoton aukuwar lamarin ga manema labarai a Bauchi, ya ce, “rahoton hatsarin mota (RTC) daga RS12.11 ya fitone daga ofishinmu da ke Azare.

Rahoton mai dauke da sa hannun Mataimakin Kwamandan da ke kula da hadura a yankin, ARC A Maga Azare, ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a ranar Litinin 15 ga watan Agustan 2022 da misalin karfe 9:07 na dare.

Yace hadarin ya ritsa da mutane da suka hada da manya maza 21 da babba mace daya, inda daga ciki maza manya tara suka rasu yayin da 13 da suka kunshi manya maza 12 da babba mace daya suka samu raunuka daban-daban”.

Rahoton ya ce an kwashe wadanda lamarin ya ritsa da su zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Azare don yi musu magani, inda likitocin suka tabbatar da mutuwar mutane tara daga cikinsu.