Hatsarin mota ya yi ajalin mutum uku a Gombe | Aminiya

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum uku a Gombe

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki
Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki
    Rabilu Abubakar, Gombe

Mutum uku sun mutu, wasu da dama kuma sun yi rauni a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a Gombe.

A dare Laraba ne dai lamarin ya auku lokacin da burkin wata babbar mota dauke da man girki ya ki aiki a kan kwanar Unguwar Bomala.

Motar ta fito ne daga mil uku ta biyo hanyar ratse ta byepass inda ta yi taho-mu-gama da wata karamar mota kirar Peugeot 206 da da wata bas mai daukar mutum 18 da keke Napep da wasu babura.

Wakilinmu ya gane wa idonsa gawarwaki uku da wadansu mutane da aka diba ranga-ranga zuwa asibiti sakamakon raunukan da suka ji don ceto rayuwarsu.

Wadanda hatsarin ya faru a kan idonsu sun shaida wa Aminiya cewa direban motar da yaronsa babu abin da ya same su baya ga kujewar da yaron motar ya yi a hannu.

‘Yan kwana-kwana da ‘yan sanda sun kai dauki cikin gaggawa yayin da jami’an hukumar Civil Defence suka dinga kwashe wadanda suka jikkata da gawarwakin zuwa asibiti.