Hatsarin mota ya yi ajalin mutun 15 a Jigawa | Aminiya

Hatsarin mota ya yi ajalin mutun 15 a Jigawa

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki
Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki
    Ishaq Isma’il Musa

Ana fargabar mutuwar mutane 15 a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Achilafiya zuwa Karnaya da ke Karamar Hukumar ’Yan Kwashi a Jihar Jigawa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

ASP Shiisu ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon taho mu gama da wasu motocin hanya biyu suka yi yayin da daya daga cikin direbobin motocin ke biyu ya yi yunkurin kauce wa ramukan kan titi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.

A cewarsa, hatsarin wanda ya auku a tsakanin motocin samfurin Golf Wagon, nan take suka kama da wuta, inda daya daga cikin direbobin da fasinja suka kone kurmus ta yadda ba ma za a iya gane su ba.

Ana iya tuna cewa, a watan Dasumbar 2017 ce wani mummunan hatsarin mota da ya auku tsakanin wata motar dauko yashi da karamar mota ya yi ajalin mutum 15 a kauyen Garin Ciroma da ke Karamar Gagarawa ta Jihar Jigawa.