✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin Zamfarawa 7 a Osun

Motar dai ta kwace ne sannan ta yi arangama da allon talla da ke gefen titi.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Osun ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai a wani hatsarin mota da ya afku a kan babban titin Ilesa zuwa Osu a Jihar ranar Laraba.

Babban Kwamandan Hukumar a Jihar, Mista Paul Okpe ne ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, a garin Osogbo.

Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 3:45 na yamma, kuma motocin na dauke da fasinjoji ne daga Jihar Zamfara.

“Wata motar bas kirar Toyota Hiace ta kwace tare da dukan allon talla, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai ta hanyar konewa,” a cewarsa.

Okpe, ya ce motar da ke dauke da babur guda da kuma fasinjoji a lokaci guda, ta karya ka’idar tuki.

Kazalika, ya ce Hukumar Kashe Gobara ta Jihar ta kai dauki wurin da hatsarin ya faru, inda suka garzaya da wanda suka ji rauni zuwa asibiti mafi kusa a yankin tare da ajiye gawar wanda suka mutu a dakin ajiye gawarwaki.

Okpe ya sake jan hankalin masu tuka ababen hawa da su kasance masu kula da kuma bin dokokin tuki.