✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauhawar Farashi: Shugaba Buhari tura fa ta kai bango

A irin wannan yanayi ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bude rumbunanta na ajiyar kayan abinci.

A ranakun 12 da 18 ga Yunin da ya gabata ne Bankin Duniya ya fitar da rahotanni kan ci gaba ko akasin haka ga tattalin arzikin kasar nan da ya saba fitarwa daga lokaci zuwa lokaci.

Dukkan rahotannin biyu, magana daya suke, wato a kan irin kuncin rayuwa da ’yan kasa suke fama da shi, wanda ya fi ta’azzara kan hauhawar farashin kayan abinci da na makamashi irin su man gas da na jirgin sama (Jet A-1) da rashin wutar lantarki da tsadarta da uwa uba tsadar abinci.

Alal misali, farashin man jirgin sama da a farkon bana yake a Naira 190 a kan kowace lita yanzu ya haura Naira 800 a kan kowace lita.

Haka labarin yake a kan man gas da yanzu ya haura Naira 800 a kan kowace lita. Man fetur an ce, ana sayarwa a kan 165 kowace lita, amma ko a cikin manyan birane ka same shi ya kai Naira 210, zuwa sama.

Hauhawar farashi a kan kayayyakin abinci irin su dawa da gero da masara da shinkafa da garin rogo da wake da burodi da kayan masarufi irin su sabulu da sukari da madara da sauransu ba a magana.

Haka labarin tsadar rayuwa da ta zama annoba a kasar nan a kan dabbobi, musamman ana batun Layya.

Babban hanzarin da masu sayar da dabbobin suke kafa hujja da shi, shi ne tsadar abincin dabbobin da kudin sufuri. Abin dai sai addu’a da neman daukin Allah.

Idan an ce da mu burodi da man fetur da dangoginsa sun karu da farashi a kan Yakin Rasha da Ukraine, kasancewar shigo da su ake daga kasashen waje, ciki har da wadancan kasashen biyu da suke gwabza yakin, sauran kayayyakin da muke sama wa a cikin gida su kuma me ke kawo hauhawar farashinsu a kullum garin Allah Ya waye, ta yadda farashin safe daban, na rana daban, haka na yamma?

Hankali zai iya gaya wa mai karatu cewa, tattalin arzikinmu, kacokan dinsa ya ta’allaka ne a kan komai shigo da shi muke daga waje.

Inda muke da masana’antun da suke iya yin wasu kayayyakin za ka tarar akasarin sinadaran da za su hada su sarrafa abin daga waje ake shigo da su.

Duk da kasar nan na cikin Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC), amma ta kasance ita ce kadai a cikin kasashen ba ta iya tace man da kasar take bukata, don haka kullum tana hanyar shigo da man fetur da dangoginsa da akasarin masana’antunmu suke matukar bukata don sarrafawa.

Ma’aikatan gwamnatocin jihohi da na tarayya da na kananan hukumomi ba su da tabbas na samun albashinsu cikakke kuma a kan kari, kasancewar kullum Gwamnatin Tarayya takan ce sai ta ciwo bashi take iya biyan albashi.

A jihohi da kananan hukumomi kuwa duk wata sai abin da hali ya yi a kan biyan ma’aikatansu albashi.

A wasu jihohin ma’aikata na bin gwamnatocinsu albashin watanni, a wasu kuma ma’aikatan ba su da tabbas na ko nawa za a biya su, sai dai abin da suka gani.

Masu karbar fansho kuwa ba a magana, bare biyan kudin sallama daga aiki, wanda a wasu jihohin sai mai yawancin rai kan karbi ladan barin aikinsa da ransa.

Rashin ingantaccen tsarin tattalin arziki da cin-hanci da rashawa da kasar nan ta dade tana fama da su, duk su suka kara jefa mu cikin tabarbarewar tattalin arzikin da muke ciki a yau.

Ma’ana, tsarin tattalin arzikinmu ya dogara ne kacokan a kan na kasashen da suka ci gaba, yayin da annobar cin-hanci take dada bunkasa.

Lokacin da muka samu damar saita abubuwa mahukuntan da suke kan mulki ba su mayar da hankali ba.

An yi lokacin da Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon yake cewa, kudi ba matsalar kasar nan ba ce, babbar matsalarta ita ce abin da za ta yi da kudin.

Ko a baya-bayan nan gwamnati tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo (1999 zuwa 2007), ta samu kudin man fetur fiye da kima, haka kudaden suka balbalce a ayyukan da ta ce ta yi wa ’yan kasa, amma kuma ’yan kasar ba su gani a kasa ba, irin su gyaran wutar lantarki da gina manyan hanyoyi.

Yanzu haka maganar da ake, dalilin yakin Rasha da Yukrain farashin danyen gangar man fetur a kasuwar duniya ya kai Dala 120, amma mahukuntan kasar nan a kullum fada mana suke cewa tallafin man fetur na cinye rarar da ake samu, don haka ’yan kasa ba za su gani a kasa ba.

Dadin-dadawa ga shi yau shekara 13, kasar nan ana fama da matsalolin tabarbarewar tsaro da ba a saba gani ba.

Ga ’yan Boko Haram da na ISWAP da Ansaru, dukkansu masu gwagwarmayar jihadi a fadarsu. Ga kuma masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da suka game kasa.

Tashe-tashen hankulan ’yan haramtacciyar kungiyar tabbatar da kasar Biyafara (IPOB) a Kudu maso Gabas, su ma suna rura annobar tabarbarewar tsaro a kasar nan. Baya ga annobar Coronavirus da ta mamaye duniya.

Dukkan wadannan matsaloli da na ambata a sama da wadanda ban iya kawowa ba, suna matukar taimakawa wajen kawo tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan da yake kara jaza wa ’yan kasa mummunan talaucin da ba su taba gani ba, wanda Allah ne kadai Ya san lokacin da za su fita daga cikinsa.

A rahotannin Bankin Duniyar ya yi hasashen cewa, nan da karshen bana mutum miliyan daya a kasar nan za su kara aukawa cikin mummunan talauci, ba ya ga sama da mutum miliyan tara da suke cikin mummunan talaucin.

A irin wannan yanayi ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bude rumbunanta na ajiyar kayan abinci don fara rabawa kyauta ko sayarwa a kan farashi mai rahusa ga ’yan kasa, ko a samu saukin tsadar awon da ake fama da shi a birni da kauye.

Masu manya da matsakaita da kananan masana’antu ma ya kamata ta waiwaye su ta hanyar inganta wutar lantarki da dukkan irin tallafin da suke bukata, ta yadda za su iya yawaita kayayyakin da suke yi, ko sa samu wadata cikin gida, har su fitar zuwa kasashen waje ta yadda za su rika samo kudaden musaya da kasar nan take matukar bukata.

Alhamdulillah! Ga damina ta sauka, manoma sun fara shuka, su ma ya kamata gwamnatoci su waiwaye su wajen wadata su da takin zamani da iri dan wuri da sauran tallafi da uwa-uba kyautata tsaro ga manoman daga farmakin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Tuni rahotanni sun tabbatar da cewa, a Jihar Neja, jihar da ta dade tana fama da farmakin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, bayan matsalolin da masu noman doya suke fama da su, ’yan bindigar, sun fara yi masu barazanar sai sun biya su wasu kudi kafin su samu zarafin yin noman bana, kamar dai yadda ’yan bindigar suka saba.