✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Hayar masu garkuwa da ni aka dauko daga Zamfara’

Sun yi alkawarin daina sana'ar tare da nadamar sace kwamishinan Jihar Neja.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar Neja, Muhammad Sani Idris, wanda ’yan bindiga suka sako bayan kwana hudu da garkuwa da shi ya ce ’yan bindigar sun yi alkawarin barin harkar.

Kwamishina Muhammad ya yi zargin ’yan bindigar ba su san shi ba ballantana inda yake zaune, amma makiyansa suka ba dauko hayarsu daga Jihar, suka kwangilar cewa idan ya ba su kudin fansa kasa da Naira miliyan 200 su hallaka shi.

Ya fadi hakan ne jim kadan bayan masu garkuwar sun sako shi a cikin da ranar Alhamis, yana mai cewa, “Na rabu da su suna kuka, na ce musu na yafe musu duniya da lahira, aboda na sa da sun sani da wallahi ba za su yi ba,

“Kuma sun yi alkawari in Allah Ya yarda Allah zai sa in zama sanadiyyar barin su sana’ar nan.

“Ba su san sunan garin nan ba, ba su san sunan karkarar nan ba, an bi su ne Zamfara an ba su kudi an ce musu kowane wata gwamna ba bani Naira miliyan 200, idan na ba su kasa da Naira miliyan 200 su halaka ni.”

Amma ya ce ya yafe musu domin, “A matsayinmu na Musulmi mun yi imani cewa Allah Ya yi alkawari cewa zai jarraba mu.

“Wadannan mutane da suka yi wannan abu, don Allah duk mai kauna ta kar ya yi musu tofin Allah-tsine, don na rabu da su suna kuka, na ce musu na yafe musu duniya da lahira.”

“Da wanda ya yi hakan, da su din, wallahi na yafe musu har abada,” inji shi.

A safiyar ranar Litinin masu garkuwa suka yi awon gaba da kwamishinan a gidansa da ke unguwar Babban-Tunga da ke kan Babbar Hanyar Abujazuwa Kaduna a Jihar Neja.

Ranar Alhamis da dare suka kira iyalansa suka sanar da su inda za su je su dauke shi a cikin dare.

Iyalan nasa da shi kansa ba su ce komai ba game da ko an biya kudin fansa.

Al’amarin garkuwa da mutane ya yi kamari a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya ya fi kamari a Neja inda a lokuta da dama aka sace dalibai masu yawa a makantu, baya ga al’ummomi da ’yan binidga suke kai wa farmaki su yi awon gaba da mutane domin karbar kudin fansa.