✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Henry Nwosu na Super Eagles ya kamu da ciwon zuciya

Shi ya fitar da Najeriya kunya a gasar Olympics a shekarar 1980.

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles Henry Nwosu na fama da rashin lafiyar da ta shafi zuciyarsa.

Hakan ta bayyana ne a lokacin da Kwamishinan Lafiya na Jihar Delta, Dakta Mordi a Ononye ya je duba shi Asibitin Kwararru na Asaba.

Kwamishinan wanda ya wakilci Gwamna Ifeanyi Okowa a ziyarar da ya kai a ranar Lahadi, ya ce gwamnatin jihar za ta yi duk abin da za ta yi wa tsohon dan wasan domin ya samu lafiya.

Ya kuma ce, ya zo dubiyar ne a madadin gwamna wanda wasu muhimman ayyuka su fitar da shi daga jihar amma da shi ne zai zo da kansa duba maras lafiya.

Henry Nwosus shi ne dan wasan tsakiya na Super Eagles wanda suka ci wa Najeriya Kofin Nahiyar Afirka a shekarar 1980.

Kuma dan kwallon shi ne wanda ya ci wa Najeriya kwallo daya tilo a gasar Olympics a shekarar 1980 wanda ya fitar da ita kunya.