✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Henry ya caccaki Wenger, Mourinho zai dauki Ndombele

Timo Werner na fuskanar kalubalen makomarsa a Chelsea.

Tsohon dan wasan Arsenal na kasar Faransa, Thierry Henry, ya caccaki tsohon kocin kungiyar, Arsene Wenger saboda shi gaba da ya yi wajen tsara gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekara bibiyu (Sun).

Kocin AS Roma, Jose Mourinho na kasar Portugal, na sha’awar kawo dan wasan tsakiya da ya horar a Tottenham, Tanguy Ndombele mai shekara 24. (Calciomercato)

Kawo yanzu Raheem Sterling mai shekara 26, na ci gaba da fuskantar rashin tabbas kan makomarsa a Manchester City. (Daily Telegraph)

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya bukaci sabon dan wasan da kungiyar ta dauko a Dortmund, Jadon Sancho da ya kara zage dantse ko hakan zai sa ya ci wa kungiyar kwallo a karon farko. (Mirror)

Everton za ta dage don ganin da dauki dan wasan Newcastle, Sean Longstaff a watan Janairu. (Independent)

Tsohon dan wasan Leipzig, Timo Werner, na fuskanar kalubalen makomarsa a Chelsea tun bayan zuwan Romelu Lukaku kungiyar a bana. (London Evening Standard)

Real Madrid za ta tanadi kudin sayen dan kwallon Borussia Dortmund, Erling Haaland a karshen kakar bana, sannan za ta ci gaba da bibiyar dan wasan PSG, Kylian Mbappe (AS Spanish)

Manchester City na duba yiwuwar dauko dan wasan Villareal, Pau Torres. (Marca)

Alex Tuanzebe da ke zaman aro a Aston Villa na son komawa zaman dindindin a kungiyar daga Manchester United. (Birmingham Mail)