✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta hana ‘Black Friday’ a Kano

Hisbah a Jihar Kano ta nemi a daina talla da sunan ‘Black Friday’.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bukaci gidan rediyon Cool FM ya dakatar da tallata garabasar kayayyaki da sunan ‘Black Friday’ wato bakar Juma’a a shirye-shiryensa.

Hukuamar ta ja hankali Cool FM cewa Juma’a rana ce mai tsarki ga jama’ar Kano, don haka take nan take ya daina amfani da sunan ‘Black Friday’.

Takardar da ta aike wa gidan rediyon dauke da sa hannun Abubakar Ali, ta ce hukumar za ta kuma sa ido a kan garabasar ‘Black Friday’ a fadin don tabbatar da bin umarnin da kawar da badala.

“Mun korafi game da shirin garabasar ‘Black Friday’ranar 27 ga Nuwamba, 2020.

“Muna jan hankalinku game amfani da sunan ‘Black Friday’ tare da sanar da ku cewa galinin mazauna Kano Musulmi ne kuma Juma’a rana ce mai tsarki a gare su.

“Don haka ake bukatar nan take ku dakatar da amfani da sunan ‘Black Friday’ kuma ku sani cewa Hukumar Hisbah za ta sanya ido wajen kawar da badala da tabbatar da zaman lafiya da kwancinyar hankali a jihar”, inji sanarwa.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ya ci tura duk da kiran wayarsa da ya yi da rubutattun sakonnin da tura masa.

Sai dai a wata ganawa da ya yi da sashen harshen Pidgin na BBC, Kwamandan Hisbah ta Jihar Kano, Shaikh Harun Ibn Sina, ya ce shawara suka ba wa gidan rediyon ya daina amfani da sunan ‘Black Friday’ amma ba hana amfani da sunan ba.

Ya ce hukumarsa ba ta da hurumin bayar umarnin hakan ga gidan rediyon.

Shaikh Ibn Sina ya ce Hisbah ta yanke shawarar sanya ido kan garabasar ne domin kar kawar da irin fitsarar da aka yi a lokacin ‘Black Friday’ na 2019.

An ruwaito Ibn Sina, na cewa wasu matasa sun yi amfani da rige-rigen sayayyar da ake yi a lokacin suna yi wa mata goge, abun da ya ce hukumar ke kyamata.