✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama giya da mata masu zaman kansu a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mota shake da kwalaben giya

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mota shake da kwalaben giya a daidai lokacin da take kokarin shiga cikin garin Kano.

Babban Kwamandan Hukumar, Dokta Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka yayin da yake tatatunawa da manema labarai a harabar hukumar.

Shaidu sun bayyana cewa sun wayi gari da ganin motar dankare da giya ne a gaban hukumar. Dokta Ibn Sina ya ce motocin uku ne dankare da giya da suka taso daga Zariya.

“Mun samu labarin motoci uku da suka taso daga Zariya wadanda kuma dukkansu cike suke da giya. Sai dai mun samu nasarar kama guda daya. Muna nan muna bin diddigin sauran biyun kuma insha Allah za mu kama su matukar za su shigo cikin garin Kano,” in ji shi.

Dokta Ibn Sina ya ce kwalaben giyar da ke cikin motar cike suke da giya ba kamar yadda ake tunanin cewa babu komai a cikinsu ba.

Ya nanata cewa dokar hana tu’ammali da giya doka ce da aka kafa a Jihar Kano karkashin Sashe na 401 wanda yake nuni da cewa sayar da giya a Kano ko shan ta ko tallata ta ko raba ta haramun ne.

A wani labarin Hukumar Hisbah ta kama mata 40 masu zaman kansu a Kasuwar Badume da ke Kano kasuwar da ta fuskanci tashin gobara a kwanan nan.

Matan wadanda suka bayyana cewa suna gudanar da sana’ar yin abinci a kasuwar ce sun nemi afuwar hukumar inda kuma suka yi alkawarin ba za su sake shiga cikin wannan hali ba.