✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama kwalaben burkutu 96 a Jigawa

An mika wanda ke sayar da giyar ga jami’an ’yan sanda

Hukumar Hisbah a Jihar Jigawa ta ce ta kama kwalaben giyar gargajiya 96 da aka fi sani da Burkutu

Hisbah ya cafke kwalaben giyar ne 96 a Karamar Hukumar Maigatari da ke Jihar, a ranar Talata.

Kwamandan hukumar a Jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne, ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), yadda suka kama kwalaben a Dutse.

Ya ce hukumar ta yi nasarar cafke kwalaben ne da misalin karfe 3:30 na dare, bayan wani samame da dakarunta suka kai wata mashayar giya.

Ya ce an kwace kwalaben ne daga wani mai suna Garba Bakule da ya yi kaurin suna wajen siyar da kayan maye.

Kwamandan ya gargadi jama’ar jihar da su guji amfani da kayan da za su iya sa su maye.

Dahiru, ya ce tuni hukumar ta mika wadanda ta cafke din ga rundunar ’yan sanda don ta mika shi ga kotu.

Kazalika, ya jinjinawa jama’ar yankin kan yadda suka bai wa hukumar hadin kai wajen gudanar da aikinta.

Kwamandan ya tabbatar da cewar Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u a fadin jihar.