✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta nemi Saudiyya ta tallafa mata wajen horar da jami’anta

Umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Hukumar Hisbar ta bakin Babban Kwamandanta, Muhammad Harun Ibn Sina ya yi rokon a ofishinsa a yayin da Hisbar ke karbar bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Aminiya ta ruwaito cewa, ayalin Limanin sun ziyarci Kano ce bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka kan ta samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su rika samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.”

Da yake mayar da jawabi Imam Albukhariy ya yaba wa Hukumar ta Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar inda ya ne msu su ribanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa Hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Bakin sun karrama Kwamandan Hisba, Ustaz Harun Ibn Sina da lambar yabo wanda ke dauke da tambarin jami’ar UmmulQurah.

A wani ci gaban kuma tawagar limaman ta kai makamanciyar wanann ziyara ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje inda kuma suka yaba masa game da hidimtawa Musulunci da yake yi a fadin jihar.

A jawabinsa, Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa dangartakar da ke tsakanin kasar Saudiyya da Jihar Kano dadaddiya ce wanda ya sanya har kasar ta Saudiyya ta bude Karamin Ofishin Jakadancinta a jihar.

A karshe, tawagar ta sanya wa Gwamna Ganduje alkyabba ’yar asali don nuna yaba wa ga ayyukan alheri da yake yi a jiharsa.