✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah ta tsare matasa 19 a wajen daurin auren jinsi a Kano

Kwamandan ya ce amarya da angon sun tsere ba a samu kama su ba.

Jami’an Hukumar Hisbah a Kano sun kama wasu matasa 19 a wajen bikin daurin auren jinsi.

Rahotanni sun nuna matasan sun hadu ne domin daura aure tsakanin wasu mutum biyu da ake zargin ’yan ludu ne.

Aminiya ta kalato cewa, jami’an Hisbah da ke aiki karkashin babban ofishin hukumar da ke Sharada, sun samu isa wurin taron a kan kari inda suka cafke mata 15 da maza hudu.

Yayin da yake tabbatar da kamen da suka yi, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Ibn Sina, ya ce sun cafke matasan ne bayan bayanan sirri da suka samu game da bikin.

Ya ce, ba su samu kama wadanda aka so daura wa auren ba sakamakon tserewa da suka yi tun kafin isan jami’ansu wurin.

Ya kara da cewa, sun kama wadda ta shirya bikin, kuma za su tsananta bincike domin kamo ango da amaryar da suka tsere.

Kwamandan ya ce, za su mika wadanda suka kama din ga ’yan sanda domin yin abin da ya dace, saboda galibin ’yan matan sun ce gayyato su aka yi.

A karshe, ya jaddada cewa Hukumar Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ayyukan masha’a da ke faruwa a fdin jihar ta Kano.