✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Hisbah ta wanke matar da ta auri saurayin ’yarta a Kano daga zargi

Hisbah ta ce matar ta cika dukkanin sharudan da Addinin Musulunci ya tanadar game da auren nata da saurayin 'yarta.

Kwamitin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kafa kan binciken auren matar da ta auri saurayin ’yarta, ya wanke ta daga zarge-zargen da ake mata.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ya fitar a Kano a ranar Talata.

Sanarwar ta ce “Gabatar da rahoton binciken da kwamiti ya ya yi karkashin jagorancin Kwamanda Malam Hussain Ahmed, an gano auren halal ta yi kuma ta cika duk wasu sharuda da addini ya tanadar.”

Sanarwar ta kuma ce bincikensu ya nuna cewar matar mijinta ya sake ta tun da fari kuma ta yi iddar wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, kafin daga bisani ta auri saurayin ’yarta da ta daina so.

Mataimakin Kwamandan ya yi watsi da zargin da ake wa matar na cewar ita ta kashe aurenta don ta auri saurayin ’yarta.

“Auren halal suka yi kamar yadda Musulunci ya tsara, shi ya sa Kwamandan Hisbah a Karamar Hukumar Rano ya jagoranci daurin auren.”

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar, Harun Ibn-Sina, ya jinjina wa kwamitin kan yadda suka gudanar da bincike tare da gudanar da aikinsu kan lamarin.

Ibn Sina ya ce hukumar ta yi nazari na tsanaki wajen zabar mambobin kwamitin duba da tarin iliminsu na Addini da kuma gogewa wajen warware matsalolin zamantakewa.

Ya gargadi jama’a da su guji yada labaran karya da fadar abin da ba su sani ba game da Musulunci.

Ya kuma bukaci al’umma da suke neman ilimi, domin Addinin Musulunci ya yi tanadin komai game da aure da abin da ya shafi iyali.

Tun da farko, Aminiya ta ruwaito yadda matar ta auri saurayin ‘yarta, wanda hakan ya sa mutane suka dinga tofa albarkacin bakinsu.

Wasu da dama sun yi Allah wadai da halin matar kan aure saurayin da diyarta ta yi soyayya da shi.