HOTUNA: Jana’izar mace mai tuka jirgin yaki ta farko a Najeriya
Thu, 23 Jul 2020 17:34:25 GMT
Kalli yadda aka yi jana’izar Tolulope Arotile, mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a Najeriya wadda ta rasu sakamakon hatsarin mota a Kaduna.
An yi jana’izar hafsar sojin saman ce a Makabartar Sojoji da ke Abuja a ranar Alhamis 23 ga Yuli, 2020.
Sojoji sun rako gawar Tolulope Arotile kafin a sanya ta a makwancinta. Hoto: Felix Onigbinde.Ministar Harakokin Mata Pauline Tallen a wurin jana’izar. Hoto: Felix Onigbinde.Yan uwanta tare da limaman addinin Kirista a lokacin jana’izar a Abuja.‘Yan uwan marigayiyar cikin alhini a wurin jana’izarta a Makabartar Sojoji da ke Abuja.Mata sojoji takwarorin Flying Officer Tolulope dauke da furanni domin bankwana gareta.Bankwana ga marigayiyar ta haryar yin harbi sau 21 bisa al’adar sojoji.‘Yar uwar Tolupe a wurin jana’izar kanwar tata.Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin yana ajiye furen bankwana da karramawa a jana’izar Tolulope.Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya hannanta tutar Najeriya ga ‘yar uwar mai rasuwar bayan an binne ta.