✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: NNPC ya fara hako mai a Nasarawa

Mele Kyari ya ce Kamfanin na kokarin yadda zai ke samar da gangar mai miliyan uku a rana.

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), ya fara hako mai a rijiyar Ebenyi da ke Jihar Nasarawa.

Babban jami’in kamfanin NNPC, Mele Kyari, a lokacin da yake magana a ranar Talata a rijiyar Ebenyi-A da ke unguwar Ajibu da ke Karamar Hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

Ya ce NNPC na bakin kokarinsa wajen kara samar da yawan man da ake hakowa a kullum daga ganga miliyan 1.6 kowace rana zuwa ganga miliyan uku a rana.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya halarci bikin fara hako man, ya ce “Yau ne aka fara aikin hako mai a Benuwai. Wannan ya yi dai-dai da sinadarin yankin Kolmani na babban titin Benuwai.”

Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka fara hako man:

Yadda NNPCL ya fara aikin hako man