✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aikin Hajjin bana ke gudana

Kalli yadda aikin Hajjin 2020 ke gudan a Masallacin Harami cikin hotuna

Laraba 29 ga Yuli, 2020 ce ranar da mahajjata da ke sauke farali a kasar Saudiyya suke fara aikin Hajji.

Ana kiran makamanciyar ranar ta 8 ga watan Zhul Hijjah a kowace shekara ranar Tarwiyya.

Ga wasu hotunan yadda alhazan ke gudanar da ibadar a Masallacin Harami a Makkah kafin su wuce su kwana a Mina sannan su karasa zuwa filin Arfa a ranar Alhamis 9 ga Zhul Hijjah:

A wurin shiga Masallacin Harami, jami’an tsaro da sauran ma’aikata na lura da alhazai.
An kawar da cunkoso, kowane alhaji na yin Dawafi ne yana bin kan layukan da aka zana a zagayen dakin Ka’abah.
Kimanin mita biyu ne tsakanin mahajjaci da na gabansa a wurin Sa’ayi tsakanin Safah da Marwa.
Alhazai sun bayar da tazara a cikin sahu suna ibada a Masallacin Harami.
Yadda alhazai ke kai komo a wurin yin Sa’ayi cikin sahu uku a tsakanin Safah da Marah.
Kalli yadda aikin Hajjin 2020 ke gudana a Masallacin Harami cikin hotuna
Wani mahajjaci yana yin addu’a bayan kammala sallar nafilar bayan Dawafi