✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

HOTUNA: Yadda aka kai wa magoya bayan Peter Obi hari a Legas

Magoya bayan Peter Obi sun zargi Jam'iyyar APC da daukar nauyin kai musu harin.

Ana zargin bata-gari sun kai wa magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi hari yayin da suke tsaka da gangamin yakin neman zabensa a yankin Lekki da ke Jihar Legas.

Maharan sun farfasa ababen hawa da dama da suka hadar da motoci da babura da ke dauke da hoton Peter Obi da mataimakinsa Dokta Yusuf Datti Baba-Ahmed.

Magoya bayan na kan hanyarsu da zuwa Filin Wasa na Tafawa Balewa da ke Legas don yin kamfe ne maharan suka far musu.

Tuni bidiyo da hotunan faruwar lamarin suka karade kafofin sada zumunta, sai dai magoya bayan Peter Obi sun zargi Jam’iyyar APC da daukar nauyin kai musu harin.

Yadda aka fasa gilashin wata babbar mota.
Yadda aka fasa gilashin wata karamar mota
Yadda aka fasa gilashin baya na wata karamar mota
Yadda gilashin wata karamar mota ya fashe