✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda karancin mai ya kawo cikas ga harkar sufuri a Abuja

Karancin man fetur din na zuwa ne bayan bayan shigo da gurbataccen mai da aka yi.

Matafiya sun yi cirko-cirko yayin da karancin man fetur ke ci gaba da ta’azzara a Birnin Tarayya, Abuja.

Karancin man fetur din ta sanya karancin ababen hawa, wanda hakan ya janyo koma baya ga harkar sufuri a Abuja.

Yadda mutane suka yi cirko-cirko suna jirana ababen hawa a garin Abuja ranar Talata. (Hoto: Abubakar Muhammad Usman).

Ma’aikata da yawa na shan wahala wajen samun abun hawan da zai kai su wajen aiki ko dawo da su.

Karancin man fetur ya sa ana kokawar samun abun hawa a garin Abuja. (Hoto: Abubakar Muhammad Usman).

Matsalar da ake fama da ita a fadin Najeriya a yanzu, ya biyo bayan gurbataccen man fetur lita miliyan 100 da kamfanin NNPC ya shigo da shi mako biyu da suka wuce.

Mutane sun yi layi a bakin titi suna jiran su samu abin hawa zuwa wuraren da za su je. (Hoto: Abubakar Muhammad Usman)