✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yadda mutane suke dafifin cirar sabbin kudi a bankuna a Kano

Wasu mutane sun koka cewar har yanzu wasu bankuna na bayar da tsofaffin kudade duk da wa'adin da CBN ya bayar.

Kwanaki bakwai kafin cikar wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar na daina amfani da tsofaffin kudi, dogayen layuka sun bulla a injinan cirar kudi na ATM a birnin Kano.

Aminiya ta gano yadda sama da mutum 50 ke bin layin cirar kudi a ATM din wasu bankuna na jihar.

Wakilinmu ya leka wasu rassan bankunan da ke kan titin Maiduguri da Murtala Muhammad Way da kewayen Sabon Gari a safiyar ranar Talata, inda ya gane wa idonsa yadda ta ke kayawa.

Sai dai har yanzu mutane na ci gaba da korafi, inda suka ce har yanzu wasu bankuna na ci gaba da bayar da tsofaffin kudi duk da umarnin da CBN ya bayar.

Yadda mutane ke bin goyon layi don cirar sabon kudi a Kano