Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu kyakkyawar tarba a yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano don ganawa da wakilan jam’iyyar a jihar.
Ga hotunan ziyarar tasa ta ranar Alhamis, 19 ga Mayu, 2022:

Tinubu a lokacin da ya sauka a Filin Firgin Sama na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano

Hadimin Shugaban Kasa Buhari kuma mai neman takarar dan Majalisar Tarayya a mazabar Gaya, Bashir Ahmad.

’Yadda masu rawan Koroso suka kayatar a lokacin da aka tarbi Tinubu a Kano.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da wasu jagororin APC a Kano

Ganduje tare da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma Sanata Barau

Tinubu a tsakanin magoya bayansa a lokacin ziyarar da ya kai Kano ranar Alhamis.

Wasu ’yan jam’iyyar APC na Jihar Kano a lokacin da Tinubu ya ziyarci jihar.

Mutane sun yi cincirindo, babu masaka tsinke a lokacin Tinubu ya kai ziyara Kano.

Dandazon mutane da suka halarci taron tarbar Tinubu a Kano.