HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano kasuwar waya inda Bene ya fado | Aminiya

HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano kasuwar waya inda Bene ya fado

    Yakubu Liman

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar gani da ido inda ginin bene ya rushe a kasuwar waya da ke Beiru Road da kuma jajantawa ’yan kasuwar dangane da abin ya faru.

Ga hotunan yadda ziyarar ta kasance:

Isowar Sarkin Kano kasuwar waya da ke titin Beirut, inda ifila’in ya faru (Hoto: Ikiramatu Suleiman)

Hakimin Fagge yana tarbar Sarki da kuma kai shi wurin da da ginin ya rushe (Hoto: Ikiramatu Suleiman)

Mai Martaba Sarki ya isa wurin da ginin ya rushe tare da duba irin barnar da ya yi. (Hoto: Ikiramatu Suleiman)

Shugaban ‘Yan Kasuwar Waya na Titin Beirut, yana yi wa Sarki bayanin yadda abin ya faru, tera da jajanta masa (Hoto: Ikiramatu Suleiman)

Daya daga ciki turawan da suke aikin bayar da agaji na gaisuwa ga sarki tare da yi masa karin bayani (Hoto: Ikiramatu Suleiman).

Sarkin Kano na yin jawabi ga ‘yan jarida a wurin da iftila’in da ya faru. (Hoto: Ikiramatu Suleiman).

Sarkin Kano na barin kasuwar bayan ziyarar gani ta gani da ido (Hoto: Ikiramatu Suleiman).