✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan bikin cikar Hadaddiyar Daular Larabawa shekara 50

Tun kafin wayewar gari aka fara gudanar da shagulgula a fadin kasar, a yayin da abokan huldar kasuwanci da gwamnatoci ke ta taya su murna.

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) na ta cika shekara 50 da kafuwa, a ranar Alhamis 2 ga watan Janairun 2021.

Tun kafin wayewar garin ranar al’umma da gwamnatin kasar suka fara gudanar da shagulgulan bikin, a yayin da abokan huldarsu na kasuwanci da gwamnatoci ke ta taya su murna.

Ga wasu daga cikin hotunan bukukuwan daga kasar:

Daliban makaratu a birnin Sharjah suna murnar bikin cikar Hadaddiyar Daular Larabawa shekara 50 da kafuwa. (Hoto: Gulf News).
Jami’an tsaron Ras al Khaimah sun gudanar da fareti a yayin bikin, wanda aka shirya kasaitaccen shagali. (Hoto: Gulf News).
A birnin Kalba a fara gudanar da bikin ne da jerin gwanon motocin ‘yan kasar, kowannesu an kayata ta da launukan tutar kasar. Manya ta yara sun fito kan tituna da cikin unguwanni domin ba wa idanunsu abinci.(Hoto: Gulf News).
Bikin cikar UAE shekara 50 ya karade kasar, inda al’ummomin kasar ke ta shagulgula tare da yin alfahari da kasar. (Hoto: Gulf News).
An yi wa gadoji da titunan birnin Abu Dhabi, hedikwatar kasar ado na musamman domin bikin cikar kasar shekara 50.(Hoto: Gulf News).
‘Yan samari ma ba a bar su baya ba wajen shiga bukukuwa a wannan rana mai matukar tarihi. (Hoto: Gulf News).

 

Masu gine-ginen kamfanoni da gidaje sun yi musu ado da tutocin kasar da alamomin nuna murnar wannan kasasitaccen biki.(Hoto: Gulf News).

 

Mata da zama, manya da kanana sun fito a sassan kasar domin yin wannan shagali da kuma kashe kwarkwatar idanunsu. (Hoto: Gulf News).

 

Wani mai wasan barkwanci yana nishadantar da ‘yan kallo a lokacin bikin. (Hoto: Gulf News).
Daga kan tituna zuwa manyan shaguna da sauran wurare, ko’ina akwai alamar wannan biki. (Hoto: Gulf News).
A nan wasu ma’aikata ne suke cashewa a wannan rana ta cikar UAE shekara 50 da kafuwa. (Hoto: Gulf News)..

 

Na wurin wani kasaitaccen baje koli ne da aka shirya a Earth Plaza a kasar a lokacin bikin. (Hoto: Gulf News).

 

 

Ma’aikatan gwamnati da abokan huldarsu suna yanka kek a ranar. (Hoto: Gulf News).

 

Alamar cikar Hadaddiyar Daukar Larabawa shekara 50. (Hoto: Gulf News).
A birnin Dubai, babbar cibiyar kasuwancin Hadaddiyar Daular Larabawa da ma duniya, an kawata kan titi da tutocin. (Hoto: Gulf News).