✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan ganawar shugabannin Fulani da Gwamnatin Ogun

Tattaunawa kan rikicin Fulani makiyaya da manoma a Gidan Gwamnatin Ogun

Shugabanin Fulani makiyaya sun isa Jihar Ogun don ganawa da mahukuntan Jihar kan matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma a jihar.

Jihar Ogun ta yi fama da rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma a kwanakin nan, tun bayan da mai taratsin kare Yarbawa Sunday Adeyemi (Sunday Igboho) ya kai wa Fulani farmaki a yankin Eguwa da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar.

Shugabannin Fulanin sun kai ziyarar ce a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Miyyeti Allah (MACBAN), Alhaji Kirwa Hardon Zuru.

Wani sashe na tawagar shugabnnin al’ummar Arewa da suka halarci tattaunwar ta ranar Talata a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.
Wasu daga cikin shugabannin Yarabawa da suka halarci zaman da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.
Tawagar shugabannin Kungiyar MACBAN sun ziyarci al’ummar Fulani makiyaya a Jihar.
Wasu Fulani makiyaya da Shugannin kungiyar suka gana da su a yayin ziyarar.
Wasu daga cikin mahalarta ganawar shugabannin Kungiyar Miyetti Allah da makiyaya.
Wasu al’ummar Arewa a kusa da jami’an tsaro da aka girke domin tabbatar da doka da oda.
Wani sashe na shugabannin al’ummar Yarabawa da suka halarci zaman da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan rikicin kabilanci da na tsakanin manoma da makiyaya a Jihar.