✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan Jana’izar Sarki Sani Kabiru na Legas

Ranar Alhamis  24 ga watan Disamba, 2020 da dare Allah Ya yi wa daya daga cikin sarakunan Jihar Legas, Sarki Sani Kabiru rasuwa. Sarki Sani…

Ranar Alhamis  24 ga watan Disamba, 2020 da dare Allah Ya yi wa daya daga cikin sarakunan Jihar Legas, Sarki Sani Kabiru rasuwa.

Sarki Sani Kabiru ya rasu yana da shekara 57 bayan  ya yi fama da jinya, an kuma yi masa sutura a ranar Juma’a a Makabartar Hausawa ta Morkaz da ke unguwar Agege a Legas.

Shaikh Tijjani Imam Khalifan Tijjaniya na Legas ne ya jagoranci jana’izar wadda kwamishinan Albarkatun Ruwa na Legas Alhaji Ahmad Kabir ya halarta.

Aminiya ta kawo maku hotunan yadda aka yi jana’izar sarki Sani Kabiru.