Hotunan zanga-zangar iyalan ’yan canji da DSS ta tsare a Kano
Iyalan 'yan canjin sun fito don nuna damuwarsu kan yadda aka tsare mazajensu.
DagaAbubakar Muhammad Usman
Wed, 2 Mar 2022 14:44:59 GMT+0100
Iyalai da ’ya’yan ’yan canjin nan da hukumar tsaro ta DSS ta tsare daga kasuwar Wapa da ke kano sun gudanar da zanga-zanga a titin gidan gwamnatin jihar kan tsare su da aka yi tsawon shekara daya.
Wasu daga cikin ’ya’yan’yan canjin da aka tsare dauke da kwalayen neman a sako iyayensu. (Hoto: Salim Ibrahim Umar, Kano).Matan ‘yan canjin tare da ‘ya’yansu sun yi tattakin neman a sako mazajensu da suka shafe shekara guda a tsare a hannun hukumar DSS. (Hoto: Salim Umar Ibrahim, Kano).‘Yan uwa da iyalai na daga cikin wadanda suka gudanar da tattakin a safiyar ranar Laraba. (Hoto: Salim Umar Ibrahim,Kano).Masu zanga-zangar sun gudanar da tattaki dauke da kwalaye zuwa layin Gidan Gwamnatin Kano. (Salim Umar Ibrahim, Kano).