✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan ziyarar Akon zuwa Zawiyyar Shaikh Ibrahim Nyass

Shahararren mawakin duniya dan asalin kasar Senegal da ke zaune a Amurka Akon, ya ziyarci Zawiyyar Fitaccen Shehun Malamin Islama Shaikh Ibrahim Nyass Kaulaha, da…

Shahararren mawakin duniya dan asalin kasar Senegal da ke zaune a Amurka Akon, ya ziyarci Zawiyyar Fitaccen Shehun Malamin Islama Shaikh Ibrahim Nyass Kaulaha, da ke kasar Sanegal.

A ‘yan kwanakin nan tauraron na wakokin R&B wanda sunansa na asali Alioune Badara Thiam ya kudiri aniyar gina katafaren birni a kasar Sanegal domin farfadowa da bunkasa al’adun Afirka a tsakanin ‘yan Nahiyar mazauna Turai; Aikin da yac e zai lakume Dalar Amurka biliyan shida.

Kungiyar matasan Darikar Tijjaniya ta Fityanul Islam ce ta sanya hoton  ziyarar da Mawaki Akon ya kai Zawiyyar a shafin ta na sada zumunta:

Alioune Badara Thiam wanda aka fi sani da Akon tare da mukarraban Zawiyyar Shaikh Ibrahim Nyass a lokacin ziyarar tasa.
Lokacin da aka karbi bakuncin Akon a Zawiyar Shaikh Ibrahim Nyass da ke Kaulaha, Senegal.
An yi wa Akon addu’a a Zawiyyar Shiakh Ibrahim Nyass.
Akon a yayin wata zantawaa a ziyararsa ga Zawiyyar Shaikh Ibrahim Nyass.