Sarkin ya je ne domin halartar bikin yaye manyan jami'an gwamnati da suka kammala kwas na 44 a cibiyar
DagaYakubu Liman
Sat, 3 Dec 2022 16:09:31 GMT+0100
Cibiyar Nazarin Tsare-tsare da Muhimman Bukatu ta Kasa (NIPPS) da ke Kuru a jihar Filato ta karbi bakunci Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Sarkin ya je ne domin halartar bikin yaye manyan jami’an gwamnati da suka kammala kwas na 44 a cibiyar.
Manyan jami’an cibiyar na maraba da Sarkin Kano a yayin ziyar. (Hoto:Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Ministan Kwadago, Chris Ngige na maraba da sarki yayin isowarsa taron. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Sarkin Kano na gabatar da jawabinsa a taron. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman)Sarkin Kano na bude wani gini da masu halartar kwas din suka inganta tare da kawatawa a cibiyar. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Sarkin Kano na duba allon shaidar kaddamar da gini da ya yi. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Jami’an shirin na zagawa da sarki cikin ginin da suka inganta da kayan aikin da suka samar (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Babban jami’in Cibiyar na yi wa sarkin kyautar girmamawa. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).Mai Martaba Sarki tare da manyan baki da kuma masu halartar kwas na 44 a cibiyar. (Hoto: Kamal Photos/Ikiramatu Suleiman).