✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kwastam ta kama buhun gawayi 1,700

Gawayin Naira miliyan 9.5 jami'an hukumar suka kama za yi fasakwurinsu.

Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama buhu 1,700 na gawayi da ake kokarin fasakwaurinsu zuwa kasashen ketare.

Kwanturolan Zone A na Hukumar Kwastam, Ahmadu Shuaibu, ya ce  kimar kudin gawayin da aka kama za a fitar daga Najeriya ta kai Naira miliyan tara da dubu dari biyar.

  1. An kama daliban Najeriya kan juyin mulkin kasar Turkiyya
  2. Daga Laraba: Wane Ne Ke Yada Labaran Karya?

Da yake nuna tarin gawayin da aka kwace a ofishin hukumar da ke Ikorodu a Jihar Legas, Shuaibu, ya ce an kama gawayin ne a wani dakin ajiya da ke Apapa, Jihar Legas.

Ya bayyana cewa doka ta haramta fitar da itatuwa da abubuwan da aka sana’anta daga gare su daga Najeriya a kokarin kasar na kare muhalli da yaki da kwararowar hamada.

A cewarsa, “Zaizayar kasa da kwararowar hamada da lalacewar kasa na daga cikin matsalolin da sare itatuwa ke haifarwa.

“Dabi’ar sare itatuwa da sunan samar da gawayi ko katakai babbar barazana ce ga al’umma.”