✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NBC ta haramta sanya wakar Ado Gwanja a rediyo da talabijin

Hukumar NBC ta ce wakar 'Warr' na kunshe da batsa da kuma tallata amfani da kayan maye

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya (NBC) ta haramta musu sanya wakar ‘Warr’ ta Ado Gwanja kan zargin lalata tarbiyya.

NBC ta ja hankalin gidajen rediyo da talabijin cewa wakar da shararren mawakin ya yi ta saba Dokar Yada Labarai ta Najeriya saboda tana nuna maye da kuma miyagun kalamai.

Hakan kuwa na zuwa ne a ranar da wasu lauyoyi a Jihar Kano suka yi karar Ado Gwanaja da wasu mawakan Arewacin Najeriya da ke tashe a kafar Tiktok a kotu bisa zargin lalata tarbiyya.

“Hukumar ta damu bisa yadda wakar Ado Gwanja ta ‘Warr’ ke tashe, duk kuwa da cewa tana cike da kalamai na rashin tarbiyya da kuma tallata yin maye.

“Abin damuwa ne ganin yadda wasu gidajen rediyo da talabijin ke sanya wakar, wanda muna kyautata zaton ba su saurari wakar da kyau kafin su fa sanyawa a tashoshinsu ba,” inji sanarwar.

Ta ba da misali da cewa baya ga nuna yadda ake yin tangadi a cikin wakar, akwai kalamai na rashin tarbiyya a cikin wasu baitocin wakar.

Ta ce, daga cikin baitocin akwai inda mawakin ke cewa, “…kafin a san mu ai mun ci kashin ubanmu…ko kin zo da hodarki ubanku zan ci, warr… Kowa ya ce zai hana mu ubansa zan ci.”

Sashe na 3.38.2c na Dokar Yada Labarai ta Najeriya ta tanadi cewa, “Wajibi ne gidan rediyo ko talabijin ya tabbata ya nuna sanin ya kamata a irin shirye-shiryen da yake gabatar wa al’umma.”

Ita dai wannan waka ta ‘Warr’ da Ado Gwanja ya yi, da wasu wakokinsa ba baya-bayan nan sun jawo tofin Allah tsine, musamman daga malaman addinin Musulunci da masu nuna damuwa kan yanayin tarbiyya.

Yawancin suna nuna damuwa ne kan abin da suka kira kalaman rashin mutunci da batsa da ke cikin wakokin, musamman ganin yadda wakokin ke tashe da kuma yadda matasa ke kwaikoyonta da yin rawarta da salo iri kafafen sada zumunta.

Idan ba a manta ba Aminiya ta kawo rahoto cewa wasu lauyoyi a Jihar Kano sun maka Ado Gwanja a  gaban kotun Shari’ar Musulunci, bisa zargin wakarsa da bata tarbiyya.

Ado Gwamna da Safiyya wadda aka fi sani da Safara’u tare da abokin wakanta Sanusi Oscar 442 na daga cikin jerin mawakan Arewacin Najeriya da ke tashe a kafar Tiktok da lauyoyin suka yi kara bisa zargin lalata tarbiyya.

Sauran sun hada da da wata fitacciyar ma’abociyar Tik Tok, Murja Ibrahim Kunya, Dan Maraya da Amude Booth da Kawu Dan Sarki  da Ado Gwanja, da Murja Kunya, sai kuma Ummi Shakira da Samha Inuwa da kuma Babiyana.

Ko a kwanakin baya, shirin Wata Sabuwa da Aminiya ke gabatarwa ya kawo rahoton yadda Hukumar Tace fina-finai ta Jihar take neman Safara’u da Sanusi Oscar 442 bisa zargin wakokinsu da lalata tarbiyya.