✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NBC ta janye dakatarwar da ta yi wa kafofin labarai

A ranar 19 ga watan Agustan ne NBC ta kwace lasisin kafofin yada labarai sama da 50.

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta Najeriya (NBC) ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu kafofin yada labaran kasar saboda gaza sabunta lasisinsu.

Darakta Janar na Hukumar, Malam Balarabe Shehu Ilelah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a a Abuja.

Ana iya tuna cewa, a ranar Juma’a, 19 ga watan Agustan 2022 ne NBC ta sanar da kwace lasisin kafofin yada labarai sama da 50, ciki har da kafar sadarwa ta Kamfanin DAAR da Rhythm FM da gidan talabijin na Silverbird , saboda bashin da take bin su na sama da Naira biliyan 2.6.

Matakin ya jawo suka ga hukumar wadda a kwanan nan ta ci tarar kafar labarai ta Media Trust naira miliyan biyar da wasu kamfanonin tauraron dan Adam kan fim din da suka haska game da ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara.

Ilelah ya ce ya samu kyakkyawan martani daga tashoshin yada labaran da ba su sabunta lasisin nasu ba, wanda ya hada da manyan kafofin yada labarai cikin kasar.

“Bayan tattaunawa da jagororin kungiyar masu kafofin yada labarai da kuma sauran masu ruwa da tsaki a bangaren, mun dauki matakin dakatar da bukatar rufe wasu gidajen labaran a fadin kasar.” in ji Ilelah.